Check out the new design

ការបកប្រែអត្ថន័យគួរអាន - ការបកប្រែជាភាសាhausa- អាពូពេីកេីរ​ ជូមុី * - សន្ទស្សន៍នៃការបកប្រែ

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

ការបកប្រែអត្ថន័យ ជំពូក​: អាល់ហុិជរ៍   អាយ៉ាត់:
قَالَ هَٰٓؤُلَآءِ بَنَاتِيٓ إِن كُنتُمۡ فَٰعِلِينَ
Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna[1] idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
[1] Yanã nufin mãtan garin, dõmin Annabin mutãne shĩ ne ubansu.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
لَعَمۡرُكَ إِنَّهُمۡ لَفِي سَكۡرَتِهِمۡ يَعۡمَهُونَ
Rantsuwa da[1] rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.
[1] Allah Yã yi rantsuwã da rãyuwar Annabi Muhammadu, tsĩrã da amincin Allah su tabbata a gare shi. Wannan shĩ ne matuƙar girmamãwar wadda Allah Yake yi wa mutum. Kuma yanã nũna cewa rãyuwar Annabi tanã da muhimmanci ƙwarai.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ مُشۡرِقِينَ
Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
فَجَعَلۡنَا عَٰلِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ حِجَارَةٗ مِّن سِجِّيلٍ
Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡمُتَوَسِّمِينَ
Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَإِنَّهَا لَبِسَبِيلٖ مُّقِيمٍ
Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.[1]
[1] Hanya tabbatacciya ta mutãnen Makka zuwa Syria (Sham).
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ
Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَإِن كَانَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأَيۡكَةِ لَظَٰلِمِينَ
Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika[1] sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!
[1] Ma'abũta Al'aika, sũ ne mutãnen shu'aibu.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
فَٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡ وَإِنَّهُمَا لَبِإِمَامٖ مُّبِينٖ
Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَلَقَدۡ كَذَّبَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡحِجۡرِ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri[1] sun ƙaryata Manzanni.
[1] Ma'abũta Hijiri, sũ ne samũdãwa.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَءَاتَيۡنَٰهُمۡ ءَايَٰتِنَا فَكَانُواْ عَنۡهَا مُعۡرِضِينَ
Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَكَانُواْ يَنۡحِتُونَ مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتًا ءَامِنِينَ
Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ مُصۡبِحِينَ
Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga Asuba.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَإِنَّ ٱلسَّاعَةَ لَأٓتِيَةٞۖ فَٱصۡفَحِ ٱلصَّفۡحَ ٱلۡجَمِيلَ
Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلۡخَلَّٰقُ ٱلۡعَلِيمُ
Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَٰكَ سَبۡعٗا مِّنَ ٱلۡمَثَانِي وَٱلۡقُرۡءَانَ ٱلۡعَظِيمَ
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗan da ake maimaita karatunsu[1] da Alƙur'ãni mai girma.
[1] Bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu su ne Fãtiha mai ãyõyi bakwai. Anã karanta su a cikin kõwace raka'a ta salla.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
لَا تَمُدَّنَّ عَيۡنَيۡكَ إِلَىٰ مَا مَتَّعۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّنۡهُمۡ وَلَا تَحۡزَنۡ عَلَيۡهِمۡ وَٱخۡفِضۡ جَنَاحَكَ لِلۡمُؤۡمِنِينَ
Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَقُلۡ إِنِّيٓ أَنَا ٱلنَّذِيرُ ٱلۡمُبِينُ
Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyanan ne."
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
كَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَى ٱلۡمُقۡتَسِمِينَ
Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,[1]
[1] Mãsu rantsuwa a kan sãɓa wa Annabãwa, watau kamar sun yi rantsuwa wa bã zã su bi abin da Annabãwa suka zoda shi ba. Wãtau su ne mãsu tsananin izgili da Addini.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
 
ការបកប្រែអត្ថន័យ ជំពូក​: អាល់ហុិជរ៍
សន្ទស្សន៍នៃជំពូក លេខ​ទំព័រ
 
ការបកប្រែអត្ថន័យគួរអាន - ការបកប្រែជាភាសាhausa- អាពូពេីកេីរ​ ជូមុី - សន្ទស្សន៍នៃការបកប្រែ

បានបកប្រែដោយលោកអាពូប៊ើកើរ ម៉ះម៉ូទ ជូមុី។ ត្រូវបានអភិវឌ្ឍន៍ដោយការត្រួតពិនិត្យពីមជ្ឍមណ្ឌលបកប្រែរ៉ូវ៉ាទ ការបកប្រែដើមអាចចូលមើលបានក្នុងគោលបំណងផ្តល់យោបល់ វាយតម្លៃ និងអភិវឌ្ឍន៍បន្ត។

បិទ