Check out the new design

ការបកប្រែអត្ថន័យគួរអាន - ការបកប្រែជាភាសាhausa- អាពូពេីកេីរ​ ជូមុី * - សន្ទស្សន៍នៃការបកប្រែ

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

ការបកប្រែអត្ថន័យ ជំពូក​: អាល់ហុិជរ៍   អាយ៉ាត់:

Alhijr

الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ وَقُرۡءَانٖ مُّبِينٖ
A. L̃.R. Waɗan can ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
رُّبَمَا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ كَانُواْ مُسۡلِمِينَ
Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.[1]
[1] Kõwane kãfiri yanã gũrin yã zama Musulmi dõmin abin da yake gani na shiriya da ladubban Musulunci, waɗanda ya tabbata bãbu zama lãfiya ga mutum fãce idan yã sãme su, amma shaiɗan yanã hana shi musulunta sabõda waɗansu dalĩlai da yake sanyãwa a ganinsa.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
ذَرۡهُمۡ يَأۡكُلُواْ وَيَتَمَتَّعُواْ وَيُلۡهِهِمُ ٱلۡأَمَلُۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ
Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَمَآ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةٍ إِلَّا وَلَهَا كِتَابٞ مَّعۡلُومٞ
Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
مَّا تَسۡبِقُ مِنۡ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ
Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَقَالُواْ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِي نُزِّلَ عَلَيۡهِ ٱلذِّكۡرُ إِنَّكَ لَمَجۡنُونٞ
Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
لَّوۡمَا تَأۡتِينَا بِٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
"Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?"
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
مَا نُنَزِّلُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَمَا كَانُوٓاْ إِذٗا مُّنظَرِينَ
Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya,[1] bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.
[1] Gaskiya a nan anã nufin azãba dõmin zuwanta tabbatacce ne. Dukan abin da yake tabbatacce shĩ ne haƙƙun, watau gaskiya.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
إِنَّا نَحۡنُ نَزَّلۡنَا ٱلذِّكۡرَ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ
Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ فِي شِيَعِ ٱلۡأَوَّلِينَ
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãnin ka.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
كَذَٰلِكَ نَسۡلُكُهُۥ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Kamar wancan ne Muke shigar da shi[1] a cikin zukãtan mãsu laifi.
[1] Shirki da kãfirci da ƙaryatãwa, su duka izgili ne da addini.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
لَا يُؤۡمِنُونَ بِهِۦ وَقَدۡ خَلَتۡ سُنَّةُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Bã su yin ĩmãni da shi,(4( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige[1] .
[1] Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Hanyar mutãnen farko ta ƙaryata Manzanni har a lõkacin da Allah zai halaka su da azãbarsa.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
وَلَوۡ فَتَحۡنَا عَلَيۡهِم بَابٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فَظَلُّواْ فِيهِ يَعۡرُجُونَ
Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
لَقَالُوٓاْ إِنَّمَا سُكِّرَتۡ أَبۡصَٰرُنَا بَلۡ نَحۡنُ قَوۡمٞ مَّسۡحُورُونَ
Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."
តាហ្វសៀរជាភាសា​អារ៉ាប់ជាច្រេីន:
 
ការបកប្រែអត្ថន័យ ជំពូក​: អាល់ហុិជរ៍
សន្ទស្សន៍នៃជំពូក លេខ​ទំព័រ
 
ការបកប្រែអត្ថន័យគួរអាន - ការបកប្រែជាភាសាhausa- អាពូពេីកេីរ​ ជូមុី - សន្ទស្សន៍នៃការបកប្រែ

បានបកប្រែដោយលោកអាពូប៊ើកើរ ម៉ះម៉ូទ ជូមុី។ ត្រូវបានអភិវឌ្ឍន៍ដោយការត្រួតពិនិត្យពីមជ្ឍមណ្ឌលបកប្រែរ៉ូវ៉ាទ ការបកប្រែដើមអាចចូលមើលបានក្នុងគោលបំណងផ្តល់យោបល់ វាយតម្លៃ និងអភិវឌ្ឍន៍បន្ត។

បិទ