Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, zã mu shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada bisa ga wa'adin Allah tabbatacce. Wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga magana?
(Al'amari) bai zama gũrace- gũracenku ba, kuma[1] ba gũrace- gũracen Mutãnen Littãfi ba ne. Wanda ya aikata mummunan aiki zã a sãka masa da shi kuma bã zai sãmi wani masõyi ba, baicin Allah, kuma bã zai sãmi mataimaki ba.
[1] Addini bã tatsuniyar baki bane, aiki ne, ko mutum ya yi mugu ya shĩga Wuta, ko kuma ya yi na ƙwarai ya shiga Aljanna.
Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan ƙwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhãli kuwa Yanã mũmini, to, waɗannan sunã shiga Aljanna kuma bã zã a zãlunce su da gwargwadon hancin gurtsun dabĩ no ba.
Kuma wãne ne ya fi kyau ga addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yanã mai kyautatawa kuma ya bi aƙidar Ibrãhĩm, Yanã mai karkata zuwa ga gaskiya? Allah Yã riƙi Ibrãhĩm badãɗayi.[1]
[1] Akwai kwaɗaitarwa ga cewa, wanda yake son Allah Ya so shi, to sai ya bi aƙĩda da aiki irin na Ibrãhĩma, sai Allah Ya so shi.
Kuma Allah ke da[1] (mallakar) abin da ke cikin sammai da kuma abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã kasance, a dukkan, kõme, Mai kẽwayewa.
[1] Ko da yake Allah Yã riƙi Ibrãhĩma "Khalĩl" watau masõyi, amma bai hana Ibrahĩma ya zama a cikin bãyin Allah kuma mulkinSa ba, domin yana daga cikin abin da sama da ƙasa suka ƙunsa a cikin su.
Sunã yi maka fatawa a cikin sha'anin mãtã. Ka ce: "Allah Yanã bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantãwa a kanku a cikin Littãfi, a cikin sha'anin marãyun mãtã waɗanda ba ku bã su abin da aka rubũta musu[1] (na gãdo) ba, kuma kunã kwaɗayin ku aurẽ su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yãra, da sha'anin tsayuwarku ga marãyu da ãdalci. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah Yã kasance Masani a gare shi."
[1] A cikin jahiliyya ba su bai wa yãra da mãtã gãdo. Musulunci ya sõke wannan al'ãda da ãyar gãdo, ãyã ta 11. Kuma idan akwai wata marainiya ga hannun wani tana da dũkiya, sai ya jefa mata mayafinsa domin ya hana ta auren wani namiji. Shi kuma ko ya aure ta ko kuma ya bar ta bãbu aure har ta mutu, su yi gãdon ta.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
លទ្ធផលស្វែងរក:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".