Sai malã'iku suka kirãye shi, alhãli kuwa shĩ yanã tsaye yana salla a cikin masallãci. (Suka ce), "Lalle ne Allah yana bã ka bushãra da Yahaya, alhãli yana mai gaskatãwar wata kalma daga Allah, kuma shugaba, kuma tsarkakke kuma annabi daga sãlihai."
Ya ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai sãmu a gare ni, alhãli kuwa, lalle tsũfa ya sãme ni, kuma mãtãta bakarãriya ce?" Allah ya ce, "Kamar hakan ne, Allah yana aikata abin da Yake so."
Ya ce: "Yã Ubangijinã! Ka sanya mini wata alãma!" (Allah) Ya ce "Alãmarka ita ce ba zã ka iya yi wa mutãne magana ba har yini uku face da ishãra. Sai ka ambaci Ubangijinka da yawa. Kuma ka yi tasbĩhi da marece da sãfe."
Wannan yana daga lãbarun[1] gaibi, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance ba a wurinsu a lõkacin da suke jẽfa alƙalumansu (domin ƙuri'a) wãne ne zai yi rẽnon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke ta yin husũma[2].
[1] Wannan yana daga cikin dalĩlan annabcin Annabi Muhammad, tsira da aminci su tabbata a gare shi, wajen faɗar lãbãrin abin da bai halarta ba. [2] Uwar Maryamu tã ɗauke ta, tã kai ta ga Bani kãhin ɗan Hãrũna ɗan'uwan MũSã, a lõkacin nan, sũ ne suke tsaron Baitil Muƙaddas, ta mĩka musu ita, ta ce: "Ku karɓa. Na 'yantar da ita, kuma mace mai haila bã ta shiga masallaci, kuma bã zan mayar da ita a gidanã ba." Sai suka ce: "Wannan ɗiyar limãminmu ce kuma shugaban Ƙurbãninmu." Zakariyya ya ce: "Ku bã ni ita dõmin innarta tanã tãre da ni." Su ka ce: "Rãyukanmu bã su iya barin ta ga wani." Sai suka yi ƙuri'a da alƙalumansu da suke rubũtun Attaura da su. Sai Zakariyya ya rinjãya. An ce sun tafi kõgin Urdun ne suka jefa alƙaluman nãsu, a kan cewa wanda alƙalaminsa bai bi ruwa ba, ya tsaya, shĩ ne ya rinjãya. Sai Zakariyya ya rinjãya, ga shi kuma shĩ ne shugabansu, kuma malaminsu, kuma annabinsu, sai ya sanya ta a cikin bene, a cikin masallacin sa.
A lõkacin da malã'iku suka ce "Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki bushãra da wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a dũniya da Lãhira kuma daga Makusanta.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
លទ្ធផលស្វែងរក:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".