Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu.[1] Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya.
[1] Rũhin Allah a nan, shi ne Malã'ika jibrĩla. Shĩ ne ya hũra a cikin wuyan rĩgarta, sai ta yi cikĩ da Ĩsã. Maryamu bã Annabiya ba ce, an ambace ta ne dõmin shimfiɗa ga maganar Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare Shi. Zamanta ãyã shi ne ta sãmi ɗã bãda namiji ba, kuma wanda ya yi haƙuri ga tsaron haddojin Allah, Allah zai ɗaukaka shi da ni'imar dũniya da ta Lãhira. Ɗanta ya zama ãyã sabõda magana yana yãro, da Annabci da ɗaukar haƙuri ga zartar da umurnin Allah.
Lalle ne wannan[1] ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini.
[1] Al'ummar Musulmi duka guda ce kõ da yake Annabãwansu sun zo dabam-dabam, a cikin lõkuta mãsu nĩSa tsakãninsu da harsuna dabam-dabam dõmin duk aƙĩdarsu guda ce a kan Ubangiji guda ne. Sa'an nan daga bãya waɗanda suka fita daga wannan aƙĩdar suka rarrabu ƙungiya-ƙungiya.
Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci!"
(A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin[1] da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne."
[1] Bãyin Allah sãlihai da malãiku waɗanda waɗansu mutãne suka bauta musu da tsammãnin cewa zã su cecesu daga Allah, bã zai sanya su Wuta ba sabõda ibãdar da aka yi musu, dõmin yabon Allah yã rigãyi hushinsa zuwa gare su. Bãyansu da mai bautar da wanda ake bautawar kamar gumãka da waɗansunsu, Wuta za su shiga.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
លទ្ធផលស្វែងរក:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".