Kuma wadda yake [1]a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi, kuma ta ce, "Yã rage a gare ka!" ya ce: "Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara!"
[1] Yũsufu yã shiga cikin fitinar uwar ɗãkinsa, Zalĩha. Yã mai da al'amarinsa ga Ubangijinsa wanda ya fitar da shi daga rĩjiya zuwa gidan sarautar Masar kuma Ya bã shi hukunci, watau Annabci da ilmi da Ya saukar masa na ibãda da mu'amãla. Ya sanar da shi halal da haram kuma ya sanya masa tsaro daga zunubi.
Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake.
Kuma suka yi tsẽre[1] zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce: "Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi."
[1] Idan namiji da mace sun haɗu, to, bã ya halatta ga namijin ya dõgara ga ilminsa na amanarsa, ya zauna tãre da fitinar Shaiɗan. Sabõda haka Yũsufu ya gudu, ta bĩ Shi da hãlin kãsãwar mutum ga hãlin so har bãkin kõfa. Suka haɗu da mijinta. Ta mayar da maganar rawãtsa (ƙarya) a kan Yũsufu. Shi kuma ya kãre kansa da maganar gaskiya. Sai shaida zã a nema.Tã himmantu da dũkarsa dõmin yã ƙi ya yi mata ɗã'a ga abin da take so daga gare shi alhãli yanã bãwanta, shĩ kuma yã himmantu da dũkarta dõmin ya tunkuɗe macũci. Alfãshar ita ce zina, cũtar kuwa ita ce dũka, dalĩlin Ubangijinsa shĩ ne bin sharĩ'ar Allah.
Ya ce: "Ita ce ta nẽme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida: [1]"Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata."
[1] Bãyar da shaida a kan al'ãda, mai bãyar da shaidar yanã gabãtar da ita da magana a kan Yusufu, dõmin a ganinsa tuhuma a kanta, tã fi karfi, kuma zumuntarsa da ita ba ta ɗauke shi ba ga karkatar da magana dõmin ya taimake ta.
Kuma waɗansu mãtã[1] a cikin Birnin suka ce: "Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna."
[1] Tsegumin mãtã a cikin gari da yadda mãtar Azĩz ta yi maganin tsegumin, ta hanyar yiwa mãtan liyafa. Mace bã ta kunyar mãtã 'yan'uwanta ga irin wannan fitina idan ta sãme ta, ita kaɗai, balle mãtã ga sũ duka sun kãmu a cikin tarkon da ya kãma ta. Sai ta gaya musu gaskiyar abin da ya auku a tsakãninta da Yũsufu, a bãyan ta rãma zargin da suka yi mata.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
លទ្ធផលស្វែងរក:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".